BIOGRAPHY: Takaitaccen Tarihin – Pst Markus Shawai

BIOGRAPHY: Takaitaccen Tarihin – Pst Markus Shawai

Takaitaccen Tarihi Akan Rayuwar Pst Markus Shawai

Pst Markus Shawai an haife shi a shekarar 5 December, 1969 a wani ƙauye mai suna Rafin Iyaka, da ke cikin yankin Sabuwar Kasa, a karamar hukumar Kafur, jiharmu ta Katsina, a Arewacin Najeriya. Shi cikakken ɗan kabilar Hausawa (Maguzawa) ne, waɗanda suka shahara da adon al’ada da kuma kwarewa wajen kiɗa da waka.

Rayuwar kiɗa ta Pst Markus Shawai ta fara ne tun da wuri. A shekara ta 1986, ya fara waka da kiɗan gurmi, yana yin wakoki a wuraren biki, auren gargajiya, da suna. Daga baya sai ya koma kiɗan kotso, wanda shine asalin kiɗan da ya gada daga iyayensa – alamar asalin sa da zurfafa a cikin al’adun Hausawa.

Bayan wani lokaci, Pst Markus Shawai ya tuba ya karɓi Kiristanci, kuma wannan ya sauya alkiblar wakokinsa gaba ɗaya. Ya daina wakokin duniya, sai ya mayar da wakokinsa na yabon Allah da girmamawa ga Yesu Almasihu. Tun daga lokacin, ya ci gaba da amfani da kiɗa a matsayin hanya ta bishara da ƙarfafa ruhin masu bi.

Fitattun wakokinsa sun haɗa da:

  1. Almasihu Muke Yabo
  2. Ceton Yesu Da Dadi
  3. Kirista Muyi Zaman Gaskiya
  4. Mubar Rike Juna
  5. Kaddararmu Da Rayuwarmu
  6. Yesu Mai Mutane Da Yawa
  7. Kayan Aro
  8. Mu Kare Mutuncinmu
  9. Aljanna
  10. Allah Muke Yabawa
  11. Allah Ka Gyara Mutane
  12. Lahira

Yanzu haka, Pst Markus Shawai yana ci gaba da wallafa sabbin wakoki da suka haɗa da saƙonni masu ƙarfafa gwiwa da cusa ƙaunar Allah a zukatan jama’a, ta hanyar kiɗan Hausa na gargajiya da ke ɗauke da ƙayatarwa da sauƙin fahimta. Wakokinsa sun zama wata hanya ta isar da bishara cikin nishaɗi da al’ada, kuma ya kafa gagarumar alama a harkar wakar bishara a Arewacin Najeriya.

Allah ya ƙara masa ƙarfi da basira wajen hidima.


Discover more from JS Loaded

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *